Mali ta yi barazanar rama duk wani hari kan Nijar
September 25, 2023Ministan harkokin wajen kasar, Abdoulaye Diop da ke wannan kalamin ya ce duk wani kutse da sojojin ketare za su yi wa Nijar, barazana ce kai tsaye ga zaman lafiyar Mali da ma tsaronta.
Gargadin Malin dai martani ne ga shelar da kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta yi game da yiwuwar aika dakaru zuwa Nijar, saboda sojoji sun kifar da gwamnatin zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum cikin watan Yuli.
Janar Abdourahamane Tchiani, da ke rike da mulkin soji a Nijar din ya ce zai sake mayar da kasar bisa dimukuradiyya cikin shekaru uku, abin kuma da ECOWAS din ta yi watsi da shi.
A makon jiya ne shugabannin sojojin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar kawance tsaro a tsakanin domin maganta duk wata barazana da ka iya afka wa guda daga cikin su.