An bankado almundahana a hukumar NDDC
September 3, 2021Tuni dai 'yan yankin suka fara tsokaci kan wanan bincike da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya sa a yi.
Yanzu dai bincike ya kammala, kuma badakalar da aka gano ta afku a hukumar, kama daga shekarar 2001 zuwa 2019 an nunar ko kare ba zai ci ba. Binciken ya tabbatar kadan ne babu a Naira tiriliyan shida da aka tura yankin, amma kuma babu wani abun a zo a gani a kasa a yankin.
Kusan dai asusun bankunan 362 aka gano hukumar na amfani da su, musamman wajen sace kudaden da ya kamata a yi ayyuka a yankin. A binciken dai, ayyuka 13,777 ne dai ake ganin ko dai ba a kammala su ba ko ma ba a aiwatar da su ba samsam.
Ralp Akajinwa mazaunin yankin cewa ya yi.
"Kimanin kudade haka sun balbalce ko kadan bai yi kyau ba, kuma wannan hukuma ta 'yan Niger Delta ce, 'yan kwangilar ma 'yan Niger Delta ne, don haka zargin 'yan Arewa ko ma shugaba Buhari kan ba a yi wa yankin adalci ba bai ma taso ba, lamari dai bai yi kyau ba".
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, za a yi amfani da sakamakon binciken wajen ganin an bar doka ta yi aikinta, don ganin an gyara kura-kurai da ke yin nakasu ga gudanarwar hukumar ta NDDC wajen hukunta duk wani ko wasu da aka tabbatar da hannayensu wajen kassara manufofin hukumar, da nufin ta ne raya yankin na Niger Delta cikin hanzari.
Don haka ma yanzu, an umarci da ministan shari'a na kasar da ya karbi kundin aikin binciken don bi daya bayan daya, da nufin shirya yadda za a fara gurfanar da wadanda ake zargin na da hannu wajen sama da fadin tiriliyoyin nairori da ake batun ko sama ko kasa.
Mr Bemene Tanem mazaunin yankin ne.
"Manufar hukumar shi ne samar da ci gaba a yankin, amma kawo yanzu babu wanu abu sai takaici. Kalilan mutane sun ta danne kudade, domin tiriliyan shida ba karamin kudi ba ne. Ina kuma kira ga shugaban kasa da ya hukunta duk masu hannu a ciki, kuma masu laifi a hana musu rike duk wani mukami da ma shiga harkokin siyasa a najeriya".
Tun dai fara aikin binciken hukumar, gwamnati ta sauke shugabanninta da ke da wakilcin sassan yankin na Niger Delta, lamarin kuma da bai yi wa 'yan yankin dadi ba, kuma yanzu ake ta dakon ganin shugaba Buhari ya kai ga sake nadawa.
Hukumar dai ta NDDC an kafa ta ne tun shekarar 2000 a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo, da nufin aiwatar da aikace aikacen raya yankin cikin hanzari, bayan wasu tashe-tashen hankula da 'yan yankin suka yi ta yi kan cewar an mayar da yankin gugar yasa, duk kuwa da cewar a yankin ne daukacin Najeriyar ke aikin fidda danyan man da ke rike kasar.