Ghana: Martani kan dokar hana auren jinsi
February 29, 2024Dokar dai ta na nuni da cewa duk wanda aka samu da aikata ko yin alaqa da ma su auren jinsin ko fafutukar tallata su ko ba su kariya, zai iya fuskantar zaman kaso tsawon watanni shida ko shekaru uku zuwa biyar. Abin da ake zaman jira kamin dokar ta fara aiki shi ne sa hannun shugaban kasar. Da ta ke mayar da martani kan dokar, Farfesa Audrey Gaddepko ta jami'ar Ghana ta yi tir da saka hannun da majalisar dokokin kasar ta yi a kan kudirin dokar. Sai dai yayin da Farfesa Gadjekpo ke nuna adawarta karara da wannan doka, wasu ma su sharhin na ganin kamata ya yi shugaban kasar ya yi taka tsan-tsan. Shi kuwa Abdrahman Baba Alhaji ya ce kasancewar wannan dokar ba wani hurumi ba ne na cin zarafi, kamar yadda a wakwanakin baya-bayan nan a kan shiga filayen taro da tsumagiya ana bulale mutane. Kawo yanzu dai shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo bai bayar da tabbacin abin da za a tsammata ba daga gare shi dangane da batun sahalewar tasa.