Najeriya: Yan Filato na martani kan Dariye
August 12, 2022Tun dai a ranar 14th, ga watan Afrilun wannan shekarar ce majalisar koli ta tarayyar Najeriya ta yi afuwa ga wasu yan Najeriya 159, ciki har da tsoffin gwamnoni biyu, Jolly Nyame na jihar Taraba da Joshua Dariye na jihar Filato. To sai dai tuni wasu 'yan Najeriyar suka soma nuna shakku ga ikirarin gwamnatin shugaba Buhari na yaki da cin hanci da rashawa
A jihar Filato dai tun bayan fitowar Dariye daga gidan yarin kuje, wasu jama'ar jihar musaman 'yan asalin karamar hukumar Bokkos maihaifar Dariye, suke ta bukukuwan murna.
To amma a cewar Madam Ladi sakin Dariye rashin adalci ne ga duk 'yan Najeriya dake tsare da suka aikata kananan laifuka wadanda ake cigaba da tsare su.
Wasu al'ummar jihar Filato na gani cewar sakin tsohon gwamnan bai kamata ba, don kuwa a lokacin gwamnatinsa ne jihar Filato ta fuskanci mummunan tashe tashen hankula shekarun baya, wasu kuwa cewa suke sakin Joshua Dariye lamari ne da ya chanchanta sakamakon halin da ya shiga yayin da kuma wasu ke daganta sakin tsoffin gwamnonin biyu kan lamari na siyasa tsantsa.