Najeriya: Bola Tinubu ya yi martani
December 6, 2022Zarge-zagen da ake wa Bola Ahmed Tinubun dan takarar shugaban Najeriyar karkashin jam'iyyar APC mai mulki, sun hadar da na cewa takardun karatunsa na boge ne da asalin iyayensa da ma coge a shekarunsa na haihuwa. An dai kwashe shekaru masu yawa ana yamadidi da wadannan zarge–zarge, musamman batun takardun karatun dan takarar neman shugabancin Najeriya na jamiyyar APC. Tun dai lokacin yana gwamnan jihar Lagos a shekarun 1999 maganar ke tashi tana mutuwa, inda a ganawar da ya yi a cibiyar Chatham House da ke London ta sake tasowa. Tinubun dai ya maida martnai yana mai cewa: "An haife ni 22 ga watan Maris 1952. Maganar takardun karatuna ai gaskiya ta bayyana, sun gane cewa sun bata kudinsu ne kawai. Ban taba ikirarin wani ne mahaifina ba, ni Tinubu ne na gaskiya. In suna bukatar a gudanar da binciken jinnina game da tsatson mahaifa, za su iya yi."
Tuni dai masu sharhi a kan siyasar Najeriyar ke bayyana fahimtarsu a kan martanin. Ta kai ga kiraye-kiraye na ya ja da baya da takarar tasa, inda wasu suka sake tunkarar kotu a kan batun domin amfani da karfin shari'a. To sai dai ga Bala Ibrahim jami'in yada labarai na jamiyyar APC, duka batun yarfe ne na siyasa kawai a ke yi wa Tinubun. Yin takakka zuwa cibiyar ta Chatham House ta zama al'ada ga duk masu neman takarar zama shugaban Najeriya a kowace jamiyya, abin da ya zama tamkar wata gasa a tsakaninsu. A yayin da yakin neman zabe ke kara zafi, za a sa ido a ga ko kurar zarge-zargen za ta kwanta haka nan ko kuma za ta sake tashi tun da an ji ta bakin wanda ake zargi.