1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'yan Najeriya kan kisan 'yan Shi'a a Zaria

Uwaisu Abubakar Idris/GATDecember 14, 2015

Matakan amfani da karfi da sojojin Najeriyar suka dauka wajen murkushe 'yan Shi'ar a garin na Zaria sun sanya 'yan Najeriya da dama dora ayar tambaya kan dalillan yin hakan

https://p.dw.com/p/1HNBQ
Nigeria - Kanduna
Gawarwakin 'yan Shi'a da sojojin Najeriya suka kashe a ZariaHoto: Getty Images

A Najeriya rikicin da ya faru a tsakamnin sojoji da‘yan Shia a garin Zaria wanda ya yi dalilin mutuwar mutane da dama na ci gaba da haifar da maida martani musamman daga fannin kwarraru a fannin tsaro a kasar. Shin wace illa wanna ke da ita ga harakar trsaron Najeriyar?

Kusan dai duk inda ka iske mutane biyu zuwa uku a mafi yawan biranen Najeriyar babu maganar da suke yi sai ta wannan mumunan rikici da ya faru a brnin na Zaria a tsakanin sojoji da mabiya Shi’a a cikin kasar, saboda muninsa da ma yadda ake fassara matakan da sojojin suka dauka a kan masu boren.

Masu sharhi kan harakokin tsaro na zargin yin amfani da karfin da ya wuce kima

Sanin halin rashin tsaro da Najeriya ke ciki wanda gwamnatin ke kokarin kwantar da shi abin da kwararru kan harakokin tsaro suka ce idan aka yi la'akari da cewa ta irin wannan ne fa rikicin da ake fama da shi a Arewa maso gabashin Najeriyar ya samo asali ya kai jama'a ga soma dora ayar tambaya mi ya haifar da wannan a halin yanzu, musamman a mulki na demokradiyya. Ga Mallam Kabir Adamu masanin a fanin tsaro na bayyana hatsarin da ke tattare da wannan lamari ta fanin tsaro.

Nigeria - Kanduna
'Yan Shi'a na zanga-zangar adawa da kisan danginsu a ZariaHoto: Getty Images

‘’ A yi amfani da karfi wurin murkushe laifi irin haka kuskure ne, idan muka duba a baya yanayi irin na Boko Haram ai irin wannan karfin aka yi amfani da shi, to akwai kuskure bangaren wadanda suka tare hanya da wadanda suka yi amfani da karfi. A tsarin aiki na soja akwai ka'idojin aiki na amfani da makamai ga fararen hula. Ba zai taba yiwuwa ba a gyara kuskure da laifi irin wannan. Matsalar wannan zai iya haifar da tunzuri daga su ‘yan Shi’a wadanda suka dade suna koke ana son a murkushe su da ma a kashe shugabansu’’

Kira ga gurfanar da masu hannu cikin kisan 'yan Shi'a a gaban kotun Hague

Tuni dai majalisar koli ta addinin islama ta fitar ta sanarwar da take gargadin gwamnati a kan wannan lamari da cewa akwai bukatar yin taka tsan-tsan. To sai dai Hajiya Naja’au Muhammad fitaciyyar ‘yar siyasa a Najeriya na ganin akwai matakan da suka kamata a ce an dauka domin kaucewa sake jefa Najeriya cikin wata sabuwar fitina da za ta iya kawo cikas a yunkurin samar da canji da ake yi a cikin kasar.

‘’Gwamnati ya kamata ba wai ma tace uffan ba amma wadanda suka aikata ta’asan na ba wai kawai a kamasu a yi masu hukunci irin na soja ba wannan shi ne ake kira laifin na kare dangi, dole ne a aika da su kotun kasa da kasa ta Hague. Kalubalantar da muke yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ya yi alkawarin zai yi adalci, don haka yanzu ne ya kamata ya gane cewa akwai masu mashi makarkashiya. Wannan ta’asar ita ta jefa kasar Iraqi ta kasara jefa Yemen da Syria a cikin yakin da ba ranar kare shi. Kuma mutane sun ki su fito su ce wannan abu da ake yi ba dai dai ba ne’’.

Nigeria - Kanduna
Sojojin Najeriya a fagyen fada da 'yan Shi'a a ZariaHoto: Getty Images

A lokutan baya dai amfani da karfi irin na soja ga mutane da a zahiri ake wa kallon ba su da karfi na makamai da za su kare kansu ya gamu da zargi na take hakin jama’a daga jami’an tsaron Najeriyar musamman sojoji wadanda kurwarsu ta yi kuka a kan wannan lamari.

Na yi iyakar kokarina domin jin tab akin mahukuntan Najeriyar kama daga ministan yada labaru Lai Muhammad zuwa ga kakkain shugabvan Najeriyar, amma dukkaninsu na masu ra’ayi batu ne day a shafi sojoji don haka a barsu su bada amsa da kansu. Duka kanwar j ace ga kakakin sojojin Najeriya.

A yayiinda ake ci gaba da maida murtani a kan wannan lamari da tuni ya yi muni, shin wane mataki ya dace gwamnati ta dauka? Tuni dai majalisar koli da addinin Islama ta Najeriya ta bayyana damuwa a kan lamarin tare da kira ga gwamnati ta yi hankali saboda sanin abinda irin wannan ya haifar a Najeriyar. Za’a ci gaba das a ido don jin dalilai da gwamnatin ko rundunar sojan zata bayar a kan wannan lamari da a yanzu ke daukan hankali Najeriyar da ma sauran kasashen duniya.