1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masana sun gabatar da hanyoyin maganin cutar Ebola

September 4, 2014

An gabatar da mangunguna takwas da rigakafi biyu na cutar Ebola a wajen taron masana

https://p.dw.com/p/1D6TF
Symbolbild - Ebola Forschung
Hoto: picture-alliance/dpa

An gabatar da mangunguna takwas da rigakafi biyu na cutar Ebola a wajen taron masana harkokin kiwon lafiya 200, da ke tattauna hanyoyin dakile annobar cutar a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce duk da wanan yunkurin da ake yi zai kai karshen wannan shekara ta 2014 kafin samun rigakafin da ake bukata, yayin da annobar ta cutar Ebola zuwa wannan lokaci ta kashe kusan mutane 2000 a kasashen yankin yammacin Afirka na Gini da, Saliyo da, Labariya da kuma Najeriya, yayin da aka samu wanda yake dauke da cutar a kasar Senegal.

Hukumar Lafiyar ta nunar da cewa bullar cutar a birnin Fatakwal na Najeriya ka iya bazuwa cikin hanzali, kuma zai yi wuya a dakile kamar yadda aka gani a Jihar Lagos. Hukumar Lafiyar ta Duniya ta ce ana bukatar kimanin dalar Amirka milyan 600, domin dakile cutar ta Ebola.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu