SiyasaGabas ta Tsakiya
Kin karbar 'yan gudun hijira Gaza a Masar
October 18, 2023Talla
Shugaban kasar Masar din Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana hakan ne bayan tattaunawarsa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da ke ziyara a Masar din, inda ya ce hakan zai bayar da kofar tilasta Falasdinawan da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan su fice zuwa Jordan din. Al-Sisi ya kuma dora alhakin gaza kai kayan agaji zuwa yankin Zirin Gaza da ke da mutane kimanin miliyan biyu da dubu 400, ga hare-haren da jiragen yakin Isra'ila ke kai wa mashigar Rafah da ta hada iyakar Masar da yankin na Zirin Gaza.