Za'a shigar da kayan agaji Gaza ta Masar
October 11, 2023Gaza dai wani dan karamin fili ne na gabar teku, da ya raba tsakanin arewaci da gabashin Isra'ila da kuma Masar a yankin Kudu maso Yammacin kasar, mai dauke da mutane kimanin miliyan 2.3 da ke rayuwa cikin wani yanayi da aka bayyana da "budadden kurkuku" saboda cunkoso, tun bayan da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta karbe ikon yankin a shekarar 2007.
Kairo, mai shiga tsakani a rikicin Isra'ila da Falasdinawa, ta kan yi kokarin ganin cewar bangarorin biyu sun warware rikice-rikicen kan iyakokinsu, domin ta haka ne kawai Falasdinawa za su iya samun 'yancinsu na zama kasa.
A wannan Larabar ce dai sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce dole ne a ba da izinin samar da muhimman kayayyakin ceton rai da suka hada da man fetur da abinci da ruwa zuwa cikin Gaza.