Masar ta sanar da karin farashin fetur bayan janye tallafi
October 18, 2024Wannan shi ne karo na uku da gwamnatin Masar ke kara farashin man fetur. Ma'aikatar kula da albarkatun man fetur ta Masar ta ce ta bambanta farashin kowacce lita ga abokanan huldar kasuwanci ta la'akari da irin nauyin man da mutum yake bukata kama daga Fam na Masar 13.75 kwatankwacin Naira 463 kudin Najeriya da kuma Fam 55.25 na Masar kwatankwacin Naira 514.40 kudin Najeriya sai kuma farashin man dizal na manyan motoci da ya kama Fam 13.37 na Masar wato Naira 455.37.
Karin bayani: Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya sanar da karin farashin man
Firaministan Masar Mostafa Madbouly ya ce gwamnati za ta ci gaba da yin kari daga lokaci zuwa lokaci har zuwa karshen shekara ta 2025, kasancewar gwamnati ba za ta iya ci gaba da bada tallafin man fetur ba a daidai lokacin da kayan masarufi ke tashin gwauron zabi a fadin kasar.