Al'umma da dama a jihar Katsina da ke Najeriya, sun dogara da kasuwancin albasa mai lawashi da ake nomawa da rani a matsayin hanyar samun kudin gudanar da hidindumun rayuwarsu. Sai dai 'yan kasuwar sun ce suna tafka asara saboda rashin kudi a hannun mutane kamar yadda zaku gani cikin wannan faifen bidiyo.