Masu yaki da makaman nukiliya sun lashe lambar yabo ta Nobel
October 11, 2024A ranar Juma'a ne a aka bai wa wata kungiyar da ke yaki da bazuwar makaman nukiliya mai suna Nihon Hidankyo dake kasar Japan lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2024.
Kungiyar ta kunshi mutane da suka tsira daga harin bama-baman nukiliya da Amurka ta harba kan Hiroshima da Nagasaki.
Shugaban kwamitin na Nobel Jørgen Watne Frydnes ya ce an basu lambar yabon ce ta 2024 a yayin da haramcin amfani da makaman nukiliya ke fuskantar barazana.
Karin bayani:'Yan Amurka biyu sun lashe kyautar Nobel ta likitanci
Watne ya ce kwamitin na Nobel ya yanke shawarar karrama mutanen da suka tsira daga harin ne kuma suka ci gaba da yaki da amfani da makaman nukiliya duk da radadin da suka ji da kuma wahalhalu da suka fuskanta.
Karin bayani:An bayyana zakarun Nobel na bana
Shugaban kungiyar ta Hidankyo a yankin Hiroshima Tomoyuki Mimak ya yi kwalla a yayin da aka sanar da sunan kungiyarsu a matsayin wacce ta samu lambar yabon ta 2024.