1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu zaman kashe wando na karuwa a Najeriya

Mouhamadou Awal Balarabe
June 29, 2017

Kungiyar da ke kula da halin da ma'aikata ke ciki a Najeriya ta bayyana cewar rashin aiki yi yayi munin da ba za a iya aunawa ba a kasar. Wannan matsalar na da nasaba da matsin tattalin arziki da kasar ke fama da shi..

https://p.dw.com/p/2feux
Nigeria Umwelt Müll
Hoto: DW

Cibiyar kididdiga ta kasa ta bayanna cewar adadin marasa aiki a Najeriya ya kai miliyan 12 da dubu dari biyu. Wannan matsala ta fi shafar matasa kasancewa kashi 70% na alummar kasar suna da karancin shekaru. Joy Nwanko babbar edita a Jarida Today Top News a birnin Fatakwal a Yankin Niger Delta ta ce " Durkushewar masana'antu da dama ne ya sa su rasa ayyukansu, kuma rashin ayyukan yi ya dada dagula matsalar tsaro, inda ma wasu ke ta shiga harkar satar danyen mai a Niger Delta, sannan 'yan Mata kuma na karuwanci don su ci abinci."

Akwai  matakai da gwamnatin yAPC karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta ce tana dauka don samar da guraben ayyukan yi, kama daga shirin nan na N-Power da dai sauransu. Amma kuma al'amarin kamar ana shuka dusa ne idan aka kwatanta da dimbin marasa ayyukan na yi da ke kasa.

Eco@Africa
Karancin aikin gwamnati ya sa matasa kama kananan sana'o'iHoto: DW

Comrade Idris Ibrahim Unguwar Gini da ke zama shugaban majalisar ciyar da matasa gaba a Najeriya, mai kuma bin diddigin shirin N-Power a Kasar ya ce " Akwai wasu manufofi da gwamnati ta bullo da su wadanda ke da kalubale matuka, wadda kuma hakan ya yi jallin da dama suka rasa ayyukan yi."

Wasu 'yan Najeriya na fafutukar neman ayyukan yi tun shekara da shekaru, kamar Fred Iyke da ya shekara 18 yana neman aiki. Shi kuwa Mr Thank God da ya shafe shekara goma ba tare da samun aiki ba ya ce " Na gama jami'a a shekara ta 2008, na kammala bautar kasa shekara ta 2012, ka duba shekarun yau, har yanzu ba aikin yi."

Masu lura da al'amuran yau da kullum na cewar muddin babu aikin yi musamman ga matasa a Kasa, to hakan na zaman hadari ga tattali arziki da zamantakewar Najeriya.