1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta yi tir da matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamai

October 27, 2024

Amurka ta dauki matakin csayar wa Taiwan makamai masu linzami a daidai lokacin da takun saka ke kara kamari tsakanin tsinin da China wada ke ikirarin mallakinta ne.

https://p.dw.com/p/4mHFb
China ta yi tir da matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamai
China ta yi tir da matakin Amurka na sayar wa Taiwan makamaiHoto: Chiang Ying-ying/AP Photo/picture alliance

China ta yi Allah wadai da matakin da Amurka ta dauka a ranar Juma'a da ta gabata na cefanar wa Taiwan da makamai masu linzami, tana mai cewa hakan na iya shafar alakar Beijing da Washington tare kuma da ruwa wutar rikici a yankinta. A cikin wata sanarwa ma'aikatar harkokinm wajen China ta ce matakin na Amurka ya keta yarjejiyonin hulda tsakanin Beijing da Washingtom, kana kuma Chinar za ta dauki duk matakin da ya dace don tabbatar da cikakken ikonta a yankunan da take ikirarin mallakinta ne.

Karin bayani: Chaina ta kaddamar da sabbin atisayen soji a kusa da Taiwan

A cewar cibiyar hada-hadar makamai ta Amurka cinikin makaman tsakanin Amurkar da tsibirin Taiwan ya tashi a tsabar kudi Dala biliyan 1,16, sannan kuma nan zuwa gaba majalisar dokokin Amurkar za ta yi kuri'a domin amincewa ko kuma yin watsi da matakin.

Karin bayani: Chaina na adawa da tallafin Amirka ga Taiwan

Duk da ikirarin China nai cewa Taiwan wani yanki ne na kasarta, amma Amurka ta amince da tsibirin a matsayin halastacciyar kasa, a ta wannan dalili ne ma Washington ke dasawa da Taipei a fannin taimakon soja.