Matashi mai baiwar gyaran salula a Kano
November 23, 2016A birnin Kano na Najeriya Allah ya yi wa wani matashi mai suna Akilu Bashir baiwa ta iya gyara duk wata wayar salula da ta gagari magyara a Najeriya. Matashin ya mallaki fasaha ta iya gyaran duk wata salula ta zamani dama duk wacce aka kera a shekaru 10 da suka gabata. Baya a ga horas da matasa yadda za su nakalci gyaran ire-iren wadannan wayoyin salula, yanzu haka matashin ya fara samar da karin wasu abubuwa a cikin wayoyin wato (Constructions)a turan ce da ke zama irin sa na farko a sananniyar kasuwar sayar da wayoyi da gyaransu ta Farm center a Kano.
Shi dai Akilu Bashir wanda akan takaita sunan sa da Akilu ka jira wato (please wait)a turance ya fara harkokin gyaran wayar hannu ne a lokacin da ya yi kicibis da wani bawan Allah mai suna Dan Sudan a kasuwar wayoyin hannu da ke a farm center shekaru 10 da suka gabata.
Babban dai abin alfaharin ga masu kai gyaran wayarsu gami da abokan ayyukan Akilu shi ne irin yadda matashin ya dara sa’a domin baya ga gyaran wayan yanzu haka ma har sauyawa wayar fasali yake yi wacce ake cewa Construction a turance.