1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Matashin da ya rubngumin zanen zamani

Aliyu Muhammad Waziri
June 16, 2021

Wani matashi a jihar Bauchi da ke Najeriya ya rungumi sana'ar zane na zamani da ya kan zana hoton mutane wanda ake kira da digital drawing, kuma a cewarsa sana'ar ta masa riga da wando har ma da hula.

https://p.dw.com/p/3v2hy
Europa auf einem Globus Computergrafik 3d rendering of a globe shows europe BLWS507117 Copyright x
Hoto: imago/blickwinkel

Matashin mai suna Huzaifa Abdullahi da aka fi sani da Huzaifiyya ya bayyana cewa la'akari da kalubalen rayuwa ga wanda bai tashi ya bidi na kan shi ba shi yasa ya riki sana'ar sa ta zane da muhimmanci kuma zuwa yanzu kwalliya ta biya kudin sabulu. Kuma Huzaifiyya yace ya taso ne da sha'awar zanen tun yana karami wanda shine ma abinda ya bashi kwarin gwiwa.

Matashin ya jaddada cewa daga lokacin da ya fara wannan sana'a zuwa yanzu ya samu dumbin alheri da ba zai iya zayyana su baki daya ba tunda har ya kai ga samun lambar yabo a matakin kasa kamar yadda ya yi karin haske kan irin wasu sauran nasarori da cimma sanadiyyar sana'ar tasa ta zane.

Sai dai duk da wadannan nasarori Huzaifa Abdullahi yace akwai kuma wasu matsaloli da ke ci masa tuwo a kwarya a cikin harkar tasa inda ya bayyana kalubalen kayan aiki na zamani a matsayin daya daga cikin abubuwan dake kawo masa tsaiko.

A wannan lokaci dai akasarin matasa sun fi raja'a da neman aikin gwamnati maimakon kama wata sana'a don samun farcen susa a rayuwa wanda kuma a yanzu samun aikin ya zamo tamkar turaren dan goma wannan yasa Huzaifiyya ya shawarci yan uwansa matasa da su nemi mafita ta hanyar kama sana'a domin shine mutuncinsu.

Daga karshe matashin ya bayyana cewa wani lokaci suna kokarin ganin sun koyar da matasa sana'ar amma kuma ba su cika mai da hankali ba ko daga sun zo sai kuma su tafi ba tare da sun tsaya sun koya domin su taimaki kan su ba.