HdM: Matashin da ya kera Keke-Napep
December 23, 2020Matashin mai suna Kamaluddeen da aka fi sani da KMC Encyclopedia, ya bayyana cewa sai da ya kwashe kwanaki 60 cur yana aikin hada Keke-Napep din. Ya kara da cewa bayan nazari na tsawon shekaru biyu, a bana burinsa ya cika. Akasarin jama'a musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, sai dai su gani ko su ji labarin irin wadannan ababen hawa wadanda ba sa amfani da man fetur, amma sai gashi yanzu sannu a hankali an fara samun matasa masu basira da hikima irin Encyclopedia da suka fara nuna hazakarsu.
Ko shin wadanne abubuwa ne suka banbamta Keke-Napep din Kamal da wadanda jama'a ta sani? Yaya kuma yanayin karkon keken kasancewar kowane abin hawa da irin nasa? Keken na Kamaluddeen ya kan yi aiki ne na tsawon sa'o'i 10 a lokacin da babu hasken rana. Matashin dai na mika kokon bararsa ga gwamnati da ta tallafa musu domin kara musu kwarin gwiwa kan irin baiwar da suke da ita, wadda a cewarsa kasa ma za ta iya amfana da su.