Matsalar fashi da makami a jihar Rivers
May 27, 2015Bayan dai wani shirin jin koke-koken jama'a da wata kafar rediyo mai zaman kanta a jihar ta Rivers ta yi kan matsalar tsaro, an jiyo da dama cikin wadanda akai hira da su suna bayyana koke-koken cewar masu fashi da makami da rana tsaka gagal a musamman babban Birnin jihar wato Fatakwal na addabarsu, hakan ya dada jawo hankulan mutane kan matsalar ta tsaro. Haka kuma masu halayyar satar mutane don garkuwa dasu da nufin karbar kudaden fansa, suma yanzu suna dada kaimi wajen aikata miyagun aikinnasu, duk kuwa da kokarin da jami'an tsaro ke yi na ganin bayan wannan matsala.
Bisa la'akkari dai da kafuwar tsarin raguwar kai-kawon mutane dauke da kimimin kudade na CASHLESS BANKING a turance da hukumomi a Najeriya suka fiddo, kusan ma yanzu ana ganin mafi yawan masu fashi da makamin sun karkata ga satar mutane ne don garkuwa dasu, kamar yadda wani mazaunin garuin yake cewa:
"Ni ganau ne ba jiyau ba game da satar wani matashi dan kasuwa a unguywar Borokiri ba dadewa ba, Sannan kuma shi ma ba'a jima ba an sace wata mata mai saida Farfesu da Giya a kan titin Hospital Rd duk a cikin wannan Birni na Fatakwal. Sabo da haka dai Allah ya sauwwaka".
A watan Maris da ya gabata, sai da gungun wasu 'yan fashi da ke karkashin jagorancin wata mata suka yi wa unguwar Mile 4 a daidai mahadar Agip, tare kuma da bude wuta kan mai uwa da wabi, bayan kuma dauki ba dadi da suka yi da 'yan Sanda, tare da salwantar da rayuka da jikkata mutanen da basu ji ba basu gani ba. Matsalolin fashi da makami da kuma sace-sacen mutane don garkuwa dasu, matsaloli ne da ke cikin jerin matsalolin tsaro da suka yi wa Najeriya katutu, wanda kuma babban kalubale ne ga sabuwar gwamnati mai shirin kama mulki ta APC bisa jagorancin Muhammadu Buhari.