1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Karancin man fetir ya haifar da matsaloli a Najeriya

Uwais Abubakar Idris SB)(MAB
October 28, 2022

Krancin man fetir da ake fuskanta a Abuja babban birnin Najeriya da wasu manyan birane na ci gaba da haifar da matsalolin sufuri da harkokin rayuwa.

https://p.dw.com/p/4IoMm
Najeriya layuka a gidajen man fetir a Abuja da ke Najeriya
Layukan man fetir a Abuja da ke NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

A Najeriya karancin man fetir da ake fuskanta a Abuja hedikwatar kasar da ma wasu manyan birane na ci gaba da haifar da dimbin matsaloli ga alumma da ma tattalin arzikin kasar, a dai dai lokacin da ake shiga cikin kuncin rayuwa a dalilin wannan matsala.

Kimanin wata guda ke nan dai Abuja fadar gwamnatin Najeriya na fama da karancin man fetir, matsalar da ta haifar da dogayen laiyyukan motoci a halilan daga cikin gidajen man da ke da man, tare da samuwar ‘yan bumburutu da ke sayar da man da dan kara tsada. Wannan ya haifara da wahalhalu masu yawa ga mutanen birnin a yayin da matsalar ke watsuwa zuwa wasu sassan kasar.

Najeriya layuka a gidajen man fetir a Abuja da ke Najeriya
Layukan man fetir a Abuja da ke NajeriyaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Karancin man fetir din na baya baya nan dai ya faro ne a dai dai lokacin da aka yi fama da mumunan ambaliyar ruwan da ta mamaye daukacin hanyar Lokoja zuwa Abuja da ta katse duk wata zirga-zirga tsakanin kudancin da arewacin Najeriya. Wannan ne dalilin da mahukuntan Najeriya suka bayyana a matsayin dalili na afkuwar matsalar. To sai dai maimakon sauki bayan janyewar ruwan abin sai kara tazara yake. Mohammed Saleh kwarre ne a fanin man fetir a Najeriya ya bayyana fahimtarsa ga lamarin.

A yayinda ta kaiga masu motoci da yawa kwana a gidajen mai a Abuja, wasu kuma sai sun wahala kafin samun man fetir din, tambayoyi mabambanta a kan dalilin ci gaba da afkuwar matsala ne cike a zukattan ‘yan Najeriya musamman mazauna birnin Abuja. To sai dai shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya bayyana cewa suna iyakar kokarinsu.

Najeriya dai ta kwashe shekaru masu yawa tana fusknatara karancin man fetir saboda gaza gyara matatun manta, abin da Mohammed Saleh ya bayyana da cewa.

Najeriya ta kasafta kasha Naira tirliyan 3.6 wajen biyan kudin tallafi a 2023, wanda ya nuna ci gaba da shigo da mai daga kasashen waje da ke jefa mutane cikin yanayi na ga koshi ga kwanan yunwa a fanin albarkar mai da kasar ke da ita.