Karancin wutar lantarki a Najeriya da Nijar
April 18, 2019Wannan matsalar daukewar wutar lantarkin dai ta saka al'umma cikin tarin matsaloli game da al'amuran rayuwarsu ta yau da kullum inda har jama'a suka fara kwana a bakin panpuna wajen neman ruwa.
Tuni dai jama'a suka fara bayyana fargabarsu da wannan matsala game da yadda zasu kasance tare da ita a cikin watan azumin Ramadan.
Wannan matsala ta karancin ruwa ta fara tsamari ne kamar yadda wasu daga cikin mazauna unguwannin kan tudu suka koka. Inda suke kwashe fiye da rabin sao'in dare ba tare da ko iska ta zo a pampunan su ba matsalar da a cewar su a shekarun baya hukumomi ke daukan ta a zaman tarifi a wanan birni da kewaye
A yanzu haka dai al'ummar birnin na Damagaram ta haura a ganga dubu 24 inda kuma a kan samu tarin jarkoki a pompunan kan layi a wurare daban daban, da suke shiga layi ko da ruwa yazo cikin dare yayin da wasu unguwannin basu ma san da ko ana wuyar ruwa ba.