1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Matsalar tsaro na yawaita

July 20, 2020

Tun bayan fashewar wani abun fashewa da ake zargin bam ne wanda ya halaka mutane shida a jihar Katsina da ke Najeriya, al'ummar jahohin Arewa maso Yammacin kasar na ci gaba da nuna fargaba.

https://p.dw.com/p/3fc6z
Nigeria Maiduguri Militär Sicherheit Anti Boko Haram 2014
Karuwar matsalar tsaro a NajeriyaHoto: picture-alliance/epa

Ba wai al'ummar jahohin shiyyar Arewa maso Yammacin Tarayyar Najeriyar ne kadai irin wannan tashin-tashina ta sanya cikin halin damuwa da rashin tabbas kan harkokin tsaron ba, al'ummar kasar baki daya musamman ma na yankin Arewa na cikin fargaba. To ko ya masana tsaro ke kallon irin jerinn hare-hare?

Manjo Bishir Galma me murabus, masanin tsaro ne a Najeriyar, kuma a cewarsa ya kamata a bincika sosai ganin cewa sojoji da dama suan mutu yayin irin wadannan hare-hare. Ya kara da cedwa ba lallai ne ace hakikanin mayakan Boko haram ne ke da hannu a kashe-kashen na yankin Arewa maso Yammaci ba, sai dai ganin yadda suke da magoya baya a yankin Afirka ta Yamma hakan mai yiwuwa ne.

Sai dai shalkwatar tsaron Najeriyar, ta ce gwiwarta ba ta yi sanyi ba kan abin da ke faruwa. a cewar Kwamanda Abdulsalam Sani na cibiyar tattara bayanai na shalkwatar tsaron. Mahukuntan Najeriyar dai sun dade suna shan alkwashin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga dadi a kasar, abin da ya zamar masu tarnaki da suka kasa warwarewa.