Najeriya: Amnesty ta ce a sa dokar ta baci kan tsaro
January 16, 2024Kungiyar ta kare hakkin jama'a Amnesty International ta nuna damuwa kan matsalar garkuwa da jama'a da ta zama babbar annoba da ke fuskantar Najeriya. Ko da a kwanakin baya sai da aka kai hare hare tare da yin garkuwa da mutane a jihohin Benue da Zamfara da kuma Abuja hedikwatar tarayyar Najeriyar. Daraktan kungiyar Amnesty a Najeriya Mallam Isa Sansui ya bayyana cewa halin da ake ciki ya sanya ‘yan Najeriya na cikin kunci.
Duk da rahotanin da ake samu na yawaitar garkuwa da jama'a, akwai hare-hare da dama da ba'a jin labarinsu saboda nisan wuraren da abin ke faruwa da kuma halin wadanda abin ya shafa ke shiga. Masana a harkar tsaro sun bayana cewa a shekarar 2023 sama da mutane 9,000 aka yi garkuwa da su a Najeriya, yayin da a watan Disamba kadai wadanda aka yi garkuwa da su suka kai sama da mutum 800. Tuni ministan kula da birnin Abuja Nyesom Wike ya kira taron gaggawa da manyan jami'an tsaro kan matsalar.
Yawaitar faruwar lamarin a Abuja hedikwatar Najeriya ya sanya damuwa sanin cewa birnin da a baya ake wa kalon tudun mun tsira, amma wannan ya sauya musamman a yankunan da ke gefen birnin na Abuja. .
Kwararru a fanin tsaro na nuna bukatar hada hannu tsakanin alummar kasar da jami'an tsaro don shawo kan matsalar tare da bayyana hadarin da ke tattare da ci gaba da biyan kudin fansa wanda gwamnati ta ce babban laifi ne.