1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar zaben shugaban kasa a Ukraine

April 17, 2014

Mahukuntan Ukraine sun zargi kasar Rasha da kokari na gani ta dagula mata lamura gabannin zabe shugaban kasar da za a yi a kasar.

https://p.dw.com/p/1BkIF
Ukraine Wahlen
Hoto: DW

Ukraine ta ce Rasha na yin amfani da tashin hankalin da gabashin kasar ke fuskanta wajen ganin ta yi kafar ungulu ga zaben shugaban kasar da za a gudanar a Ukraine din cikin watan mai kamawa.

Firaministan Ukraine mai rikon kwarya Arseny Yatseniuk ne ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi da manema labarai a birnin Kiev, inda ya ke cewar kasarsa ba za ta lamunci haka ba kuma za ta yi bakin kokarinta wajen ganin komai ya tafi daidai.

Kalaman na Mr. Yatseniuk dai na zuwa ne bayan da shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce irin tsarin da ake bi wajen yakin neman zabe a Ukraine din ya saba ka'ida kuma Moscow ba za ta taba amincewa da sakamakon zaben da za a samu ba muddin aka cigaba a kan irin tsarin da ake.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu