Matsalolin tsaro sun ta'azzara a yankin arewacin Najeriya
December 10, 2021Mutane da dama a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yamamcin Najeriya na ci gaba da tattaunawa da 'yan bindiga da nufin ba su makudan kudade dan su bar su zauna lafia. Yanzu haka akwai wadanda suka biya kudaden akwai wadanda kuma suke kan tattaunawa. Yankin 'yan Biki da ke karamar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara na daga cikin yankunan da yanzu haka ke kan teburin sulhu da 'yan bindigar, saboda su bar su, su zauna lafiya ba tare da sa bakin Mahukunta ba kamar yadda mazaunin yankin ya shaidama DW.
Sai dai akwai wasu garuruwa a karamar hukumar Tsafe da aka sanya wa irin wannan haraji na milliyoyin nairori Kuma suka biya amma hakan baisa maharan sun bar sun sararaba sun cigaba da tatikarsu ga abun wani daga cikin garuruwan da suka bada kudin ke cewa duk Wanda baiso a ambaci sunansa ba. Itama Karamar hukumar Shinkafi dake jihar ta Zamfara na cikin wannan yanayi inda harma sun fara yin mubayi'a ga lamarin
Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta musanta sasanci da ake da 'yan bindigar Kamar yadda kakakin ta SP Shehu Muhammad ya bayyana.