1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsaya kan kafa gwamnatin hadaka a Jamus

Abdul-raheem Hassan
February 8, 2018

Shugabannin jam'iyun CDU ta 'yan mazan jiya da jam'iyar SPD ta masu sassaucin ra'ayi a Jamus, sun cimma matakin karshe na kafa gwamnatin gamin gambiza.

https://p.dw.com/p/2sKXX
Koalitionsverhandlungen von Union und SPD Schulz Seehofer Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Wannan mataki na jam'iyyun ya biyo bayan jerin tattaunawa da dama da aka gaza cimma fahimtar juna, abinda ake ganin baya rasa nasaba da cimma amincewa a kan wasu bukatun dukkanin jam'iyun. Sai dai a wannan loakci ana ganin jam'iyyun biyu sun samu fahimta kan wasu kudurori da suka hada da rabon mukamai a gwamnati domin samun damar yin aiki tare.

Jam'iyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wato CDU, ta shiga wani yanayi na rashin tabbas, tun bayan rashin samun gagarumar rinjaye a zaben 'yan majalisu. Rashin samun yawan wakilai a majalisar ya haifarwa jam'iyar nakaso na rashin kafa gwamnati tu bayan babban zaben kasar da aka gudanar a watan Satumban shekara ta 2017.