1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayar Jamus kan yunkurin kama Netanyahu

May 24, 2024

Barazanar kama shugabannin Isra'ila da kotun duniya ta ICC ta yi ta haddasa zazzafar muhawara a tsakanin 'yan siyasar Jamus.

https://p.dw.com/p/4gGNW
Hoto: Matthias Rietschel/REUTERS

Isra'ila ta shiga babban bacin rai kan matakin babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Karim Khan. Mr. Khan, ba wai kawai ya nemi a ba shi sammacin kama wasu shugabannin Hamas ba saboda zargin aikata laifukan yaki tun bayan harin ta'addancin da Hamas ta kai wa Isra'ila a watan Oktoba ba, ya nemi a ba shi sammacin kama firaministan Isra'ila Netanyahuda ministan tsaronsa. An kuma samu martani da yawa. Shugaban Amurka Joe Biden ya goyi bayan Isra'ila, yayin da Faransa ta kare kotun hukunta manyan laifukan ta duniya.

Mece ce matsayar Jamus?

Gwamnatin tarayyar Jamus ta mayar da martani a takaice kan batun, inda ta ce kotun hukunta manyan laifuka ta kasance babbar nasara ga al'ummar duniya, in ji wata rubutacciyar sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen kasar a karshen mako. A kodayaushe Jamus na goyon bayan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da kuma mutunta 'yancin kai.

Sai kuma wani sharhi mai muhimmanci, wanda, duk da haka, ba ya nufin ainihin zarge-zargen, amma ga neman sammacin kama shugabannin Hamas da mambobin gwamnatin Isra'ila, ciki har da Netanyahu. A cewar Ofishin Harkokin Waje Jamus, wannan ya ba da ra'ayi mara kyau na daidaito. Sai dai ma'aikatar harkokin wajen ta Jamus ta soki yadda aka dai-daita shugabannin Isra'ila da na Hamas.

Jam'iyyar adawa ta CDU, martaninta ya kasance cikin taka-tsantsan bisa matakin na aika sammaci wa shugabannin Isra'ila,

''Dai-daikun aikata laifin yaki na iya auku daga dukkan bangarorin. Sai dai shin ko shugabannin ne suka ba da umurnin yin hakan? Wannan shi ne zargin da babban mai gabatar da kara ya yi, wannan a iya sani na bazan iya tabbatarwa ba'' in ji mai kula da harkokin wajen jam'iyyar Jürgen Hardt.

Akwai dai bambancin tsakanin aikata laifin yaki da ake zargin kasar Siriya da kuma Falasdinawa, domin ita Siriya ba ta cikin kasashen da suka amince da kotun ta hukunta manyan laifuka. Amma dai bayan amincewa da bukatar babban mai shigar da karar daga alkalan kotun, to ya zama wajibi ga dukkan kasashen da suka sa hannun yarjejeniyar kotun, su kama firaministan Isra'ila Benjamin Netanhu idan ya shigo kasashensu ciki kuwa har da Jamus dole ta kama shi kuma ta mika shi ga kotun wace ke a birnin The Hague.