Matsayin Jamus game da shirye-shiryen nukiliyan Iran.
May 11, 2006A daidai lokacin da ake ce-ce ku ce a fagen siyasar ƙasa da ƙasa game da batun shirye-shiryen makamashin nukiliyan da Iran ta sanya a gaba, jami’an tsaron Jamus na nan na ta ba ƙaimi wajen binciken wasu kamfanoni a nan ƙasar, waɗanda ake tuhumarsu da sayar wa Iran ɗin na’urorin gina cibiyoyin makamashin nukiliyanta da ake ƙorafi a kansu a halin yanzu. A cikin ’yan makwanni da suka wuce, ’yan sanda sun yi ɗauki a kamfanoni 44 a duk faɗin tarayya, wai don neman hujjoji dangane da tuhumar da suka yi wa kamfanonin. Amma bisa rahotannin da suka biyo bayan wannan ɗaukin, babu wani muhimmin abin da jami’an tsaron suka gano. Sai dai tashoshin talabijin sun gabatad da wani shiri, inda suka ambaci wata ganawar da aka yi a asirce, da kamfanonin Jamus suka yi da wasu jami’an ƙasar Iran, a shekarun baya. Ɗaya daga cikin waɗanda suka sayar wa jami’an na’urori na huskantar shari’a yanzu a birnin Mannheim.
Mahukuntan Jamus dai, tun ’yan shekarun bayan nan ne suka ba da ƙaimi wajen fatattakar masu sayar wa ƙasashen ƙetare na’urorin masana’antun nukiliya. Ba abin mamaki ba ne kuwa, da Jamus ɗin take sahun gaba, cikin masu adawa da shirin makamashin nukiliyan Iran. Game da irin rawar da Jamus ke takawa a fafutukar da ake yi na hana yaɗuwar fasahar makamashin nukiliya a duniya, Mark Hibbs, wani shahararren masani a fannin wannan fasahar, wanda a halin yanzu yake zaune a Bonn, ya bayyana cewa:-
„A cikin shekarun 1990 ne Jamus ta sake salonta. Mun san dai cewa, a cikin shekarun 1980, masana’antun Jamus sun yi amfani da sassaucin dokoki a wannan lokacin, wajen sayar wa wasu ƙasashe na ƙetare kamarsu Iraqi kayayyaki da na’urori, waɗanda za su iya taimaka musu wajen sarrafa makaman nukiliya. Sai a cikin shekarun1990 ne, yayin da wannan harkar ta bayyana, gwamnatin Jamus ta yi katsalandan, tare da zartad da sabbin dokoki, don sa ido kan harkokin cinikin ƙetare. Ta hakan ne kuwa, aka sami ragowar kasuwancin irin waɗannan kayayyakin daga Jamus zuwa ƙasashe kamarsu Iraqi da Iran. Har ila yau dai, akwai karo da dama, inda aka gano keta waɗannan dokokin tare da hannun wasu kamfanoni na Jamus. Sai dai ba a nan Jamus ake ƙulla hulɗodin cinikin ba. Akwai dillalai a ƙetare, waɗanda ke samar wa ƙasashe kamarsu Pakistan, da Iran da Iraqi waɗannan kayayyakin. Ba haka kawai kuma ake iya gano su ba.“
Dabarar da waɗannan dillalan ke yi ita ce, sai su bi ta kan wani kamfani a Rasha su yi odar na’urori daga nan Jamus, waɗanda kuma suke samun izinin fid da su. To amma ba a Rashan na’urorin ke saura ba. Kai tsaye, ta wasu hanyoyi na sirri, sai a sulala su zuwa wasu ƙasashe, waɗanda aka hana tura musu irin waɗannan kayayyakin. To wannan ne ƙalubalen da hukumomin Jamus ke huskanta a halin yanzu. Kamar yadda Hibbs ya bayyanar:-
„A wasu lokutan, ana barazanar ɗaukaka ƙarar cin amanar ƙasa game da wasu kamfanonin da ake tuhumarsu da keta dokokin. Sai dai, abin da muke lura da shi a nan shi ne, da wuya a iya hujjanta wannan ƙarar. Sabili da haka, abin da ake yi shi ne, a zargi kamfanonin da take ƙa’idojin kasuwancin ƙetare na Jamus. To wannan zargin kuwa, ko da an sami mutum da laifi aikata shi, hukuncin da za a iya yanke masa shi ne ɗauri na shekara ɗaya ko biyu kawai a gidan yari.“