1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayin Jamus game da 'yan jaridanta a Iran

December 27, 2010

Jamus ta ce babu ƙamshin gaskiya game batun ganawar 'yan jaridan Bild am sonntag na ƙasarta da danginsu da Iran ta ce sun yi.

https://p.dw.com/p/zqSJ
Jaridar Bild am Sonntag ta JamusHoto: DW

Gawamnatin Jamus ta ƙaryata ganawa da hukumomin Iran suka ce 'yan jaridan ƙasarta da ke tsare sun yi da danginsu a kurkukun da suke tsugune. Wani jami'i da ke magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya ce manyan jami'an gwamnatin Teheran sun yi alƙawarin dubawa da idanun rahama bukatar da suka miƙa musu na barin dangin 'yan jaridan su yi ƙeƙe da ƙeƙe da su . Amma har ya zuwa yanzu, ba su isa garin Tabriz da aka tsare su 'yan jaridan ba.

kanfanin dillacin labaran Iran ne ya fara nunar da cewa 'yan jaridan sun gana da 'yan uwansu,kafi daga bisani ya kawo Gyara ga labarin da ta watsa. Waɗannan mafarauta labaran na Jamus da ke yi wa jaridar Bil am Sonntag aiki, sun shiga hannu ne sakamakon hira ba bisa ƙai'ida ba da su ka yi da lawya da kuma ɗan matar da ake neman jefewa bisa zargin kisan kai da kuma zina.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Abdullahi tanko Bala