Najeriya: ISWAP ta kashe manoma sama da 40 a Borno
January 13, 2025Wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar ISWAP ne sun kashe akalla manoma 40 a ranar Lahadi da ta gabata a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya kamar yadda mahukuntan jihar suka sanar a Litinin din nan.
A cikin wata sanarwa, kwamishinan yada labaran jihar Usman Tar ya ce mayakan kungiyar mai alaka da IS sun tara manoman da yammacin jiya Lahadi a karamar hukumar Dumba da ke gabar Tafkin Chadi inda suka bindigesu har lahira saboda saba wa dokar da suka saka ta hana noma da kamun kifi a yankin.
Galibin wadanda aka kashe manoman wake da albasa ne da suka fito daga yankin Gwoza mai iyaka da Kamaru, kuma tuni gwamnatin jihar ta umurci jami'an tsaron da ke yaki da ta'addanci da su gaggauta bin sawun 'yan ta'addar domin murkushe su.
Wata majiya a yankin ta shaida wa AFP cewa monoman da aka kashe sun zarta mutune 100, kana kuma sun fuskanci wannan hukunci ne saboda karya dokar da ISWAP ta saka musu inda suka bai wa Boko Haram kudi domin ta sahale musu yin noma a yankin.