1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mayakan tawaye sun datse zirga-zirga a arewacin Mali

December 21, 2023

Mayakan tawayen Abzinawa a Mali, sun datse wasu manyan hanyoyi a yankunan da sojoji suka bayyana samun galaba a makonnin baya a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4aQX2
'Yan tawayen Abzinawa na arewacin Mali
'Yan tawayen Abzinawa na arewacin MaliHoto: Souleymane Ag Anara/AFP

Abzinawan da ke cikin kungiyar hadaka ta tawaye, sun ce matakin datse hanyoyin ya shafi yankunan arewacin Malin ne da ke da iyaka da kasashen Moritaniya da Aljeriya da kuma Nijar.

Sanarwar da wata kungiyar da ke kiran kanta CSP ta fitar, ta yi nunin cewa abin ya shafi biranen Menaka da Kidal da Gao da Timbuktu da kuma Taoudeni.

Toshe hanyoyin na nufin dakatar da zirga-zirgar jama'a da kuma sauran kayayyakin bukatu na yau da kullum.

Mayakan tawayen na Abzinawa dai sun fuskanci turjiya daga dakarun gwamnati, inda a tsakiyar watan jiya na Nuwamba, aka kwace wasu yankunan da a baya suke rike da su a arewacin birnin Kidal.