1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Taron mazauna yankunan karkara

Salissou Boukari SB/AH
June 27, 2024

A Jamhuriyar Nijar da safiyar an buda babban zaman taron kungiyar mazauna karkara ta makyaya da manoma wadda ake sa ran za ta fitar da sabuwar makoma musamman a irin yanayin da ake ciki.

https://p.dw.com/p/4haCr
Nijar | Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki
Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkiHoto: Balima Boureima/AA/picture alliance

A Jamhuriyar Nijar da safiyar an buda babban zaman taron kungiyar mazauna karkara ta makyaya da manoma wadda ake sa ran za ta fitar da sabuwar kibla dangane da ayyukanta na ci gaban mutanen karkara ta fannoni da dama wadda kungiya ce da ta kumshi wasu manyan kungiyoyin mazauna nkarkara guda 13 da suke ayyuka a fannoni daban-daban.

Karin Bayani: Zaman makoki a Jamhuriyar Nijar

Niger Aktuelle Lage in Niamey
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP

Shi dai wannan babban taro na kungiyar da ake kira Plate – forme Paysanne, wata katafariyar kungiya ce ta mazauna karkara da suka hada da manoma da makyaya gami da masu sana'ar kifi, wadda wasu gamayyar kungiyoyi 13 da ke ayyuka a fannin raya karkara, inda uwar ta yi aiki tsawon shekaru biyar inda kungiyar ta ce duk da cewa ta na iyakar nata kokari amma kuma tilas sai fa gwamnati ta dafa muddin ana son bunkasa fannoni daban-daban na mazauna karkara.

A fuskar masu kamun kifi da suka halarci wannan taro ta bakin shugabansu Alhaji Seyni Yacouba, ya ce matsalar sauyin yanayi na haddasa babban koma baya a fannin kiwon. Gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar ta hanyar mai bai wa ministan kula da harkokin noma da kiwo na kasa shawara ta ce ta na sane da tarin matsalolin da kungiyoyin mazauna karkara suke ciki inda ta haka ne shugaban kasa ya bai wa ministan umarnin shiga lungu da sako na kasar domin sanin takamaiman halin da mazauna krkara suke ciki.

Abun jira a gani dai shine matakin da gwamnatin za ta dauka tare da wadannan manyan kungiyoyi na mazauna karkara don ganin an samu cikeken sauyi na tunani ta yadda a nan gaba noman da ake yi zai iya ciyar da yan kasa har ma a yi tunanin ciyar da wasu a fannoni da dama na abubuwan da Nijar din za ta samar.