MDD ta ja hankalin Najeriya kan 'yan Chibok
July 25, 2017Talla
Fiye da 'yan mata na makarantar Chibok 100 ne dai ke hannun mayakan na Boko Haram, bayan kwashe su kimanin 270 da suka yi cikin watan Afrilun shekara ta 2014, a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.
Wata tawagar kwararru ta bai wa MDD shawarin cewa wajibi ne a tabbatar da an bai wa mata da 'yan matan da Boko Haram ke garkuwa da su, cikakkiyar kulawar da za ta kyautata tunaninsu ta yadda za su iya sajewa da jama'a ba tare da samun matsala ba.
Sama da mutum dubu 20 ne dai tarzomar ta Boko Haram ta halaka tare da raba wasu sama da miliyan 2 da sukuni, cikin tsukin shekaru bakwai na yakin da suke ikirarin na kafa daula a nahiyar Afirka.