1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel da Schulz sun yi muhawara ta talabijin

Ahmed Salisu
September 3, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus kana jagorar jam'iyyar CDU Angela Merkel ta yi muhawara ta talabijin da wanda ke kalubalantar ta a zaben da za a yi a ranar 24 ga watan na Satumba, wato Martin Schulz na jam'iyyar SPD da ke adawa

https://p.dw.com/p/2jICa
TV-Duell Angela Merkel und Martin Schulz
Hoto: picture alliance/Dpa/dpa

Shugabannin manyan jam'iyyun kasar na SPD da CDU sun maida hankali ne a muhawarar ta su kan batutuwan da suka hada da karbar 'yan gudun hijira har ma Merkel ta ke cewar bakin da kasar ta karba ba barazana ba ce ga Jamus, sai dai duk da wannan Schulz ya caccaki Merkel kan shirinta na karbar 'yan gudun hijira wanda ya ce ya na cike da kura-kurai.

A share guda Schulz din ya amince cewar kasancewar baki musamman ma Musulmi a kasar ba zai zama wata matsala ba amma dole ne a tabbatar an dakile aikin masu cusa tsattsauran ra'ayi a kasar. Dama dai tun da fari Merkel ta bayyana cewar Musulmi wani ginshiki ne na tarayyar Jamus duba da yawan wadanda suka saje da al'ummar kasar.

Deutschland TV Duell Merkel Schulz
Merkel da Schulz sun nuna damuwa kan shirin makaman nukiliya na Koriya ta ArewaHoto: picture alliance/AP Photo/RTL

Batun shirin nukiliyar Koriya ta Arewa da kuma gwaje-gajen da ta ke yi na makamai masu linzami da ke cin dogon zango na zaman guda daga cikin abubuwan da shugabannin suka fuskanta yayin muhawarar. Da aka tambayi Martin Schulz ko ya na ganin Shugaba Trump na Amirka zai iya warware wannan matsalar sai ya kada baki ya ce duk shugaban da ke amfani da shafin Twitter wajen caccakar abokan hamayyarsa ba shi da maraba da masu ra'ayin Nazi wanda shugaba na gwamnatin Jamus ya kamata ya tashi tsaye wajen yaka. A martaninta kan wannan batu, Merkel ta ce duk da cewar suna da banbance-banbance da Trump amma ya kamata a dafawa Amirka wajen ganin ta yi amfani da matakai na diflomasiyya wajen warware takaddamarta da Koriya ta Arewa.

Da aka maida hankali kan batun shigar Turkiyya cikin kungiyar tarayyar Turai ta EU kuwa, Schulz ya ce muddin 'yan Jamus suka bashi dama ta darewa kan madafun iko to kuwa kasar za ta tsame hanneyenta daga dukannin wata tattaunawa kan wannan batu domin a cewarsa ba za su zuba idanu su bar shugaban da ke mulki irin na kama karya ya na abinda ya ga dama ba, ciki kuwa har da kamewa tare da garkame mutanen ba gaira ba dalili. Ita kuwa a nata bangaren, Merkel fitowa fili ta yi baro-baro ta bayyana cewar ba ta taba tunanin cewar Turkiyya za ta samu nasarar shiga kungiyar EU ba.