Merkel ta kare matakin dokar kulle
October 29, 2020Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kare matakin gwamnatinta na sanya kwarya kwayar dokar kulle domin dakile sake bullar cutar corona a wani jawabi da ta yiwa yan majalisar dokoki na Bundestag.
"Tace na fahimci damuwar da ake da ita musamman a wuraren da aka sanya tarnaki game da kullen. A halin da ake ciki ba mu iya gano kashi 75 cikin dari na sabbin kamun ba, a saboda haka akwai bukatar hanzarta daukar matakai domin shawo kan lamarin."
Jawabin nata ya zo a daidai lokacin da kasar ke fama da karuwar sabbin kamun cutar a kullum inda a rana guda aka sami mutane 16,700 da suka kamu da cutar.
A ganawar da ta yi a ranar laraba da gwamnonin jihohi 16 na Jamus, sun cimma matsayar sanya kwarya kwaryar matakan kulle na wata guda domin dakile yaduwar cutar ta corona a fadin kasar.