Merkel ta kare tsarinta na 'yan gudun hijira
September 7, 2016Merkel ta jaddada hakan a jawabin da ta yi gaban majalisar dokokin kasar ta Bundestag. Jawabin nata dangane da kasafin kudi, ya gudana ne kamar yadda aka saba shugaban gwamnati na zuwa gaban majalisa don bayyanan wasu manufofi. A jawabin shugabar gwamnatin Jamus din dai, ta tabo abubawa da suka hada da matsalolin cikin gida da na ketare. Jawabin nata dai ya zo ne kasa da mako guda bayan mummunan kayen da jam'iyarta ta CDU ta sha a zaben kanan hukuomi na jiharta, inda jam'iyar AfD ta masu tsananin kin baki ta samu gagarumar nasara. Wannan dai ya sa Angela Merkel yin gargadi ga 'yan kasarta su yi hattara da masu ra'ayin kyamar baki.
Duk da cewa yarjejeniyar kasashen Turai kan dakile kwararar baki wadda suka cimma da kasar Turkiya a yanzu tana tangal-tangal, Merkel ta dage cewa hakan shi ne kadai mafita. Ko da yake akwai Jamusawa da yawa musamman 'yan siyasa da ke zargin kasashen Turai musamman gwamnatin ta Jamus da kawar da ido bisa irin take hakkin dan Adam wanda gwamnatin Turkiyan ke yi, sai dai shugabar gwamnatin Jamus ta kare kanta tana mai cewa:
"Ina fada muku a nan cewa, ina sake jadda muku, idan Turkiya ta take hakkin jama’a muna fada mata gaskiya. Lokacin da yunkurin juyin mulkin sojoji a Turkiya bai yi nasara ba, mun ce hakan ya yi dai-dai yadda jama’ar kasar suka kare gwamnati ta hanyar fitowa kan titina domin nuna tirjiya."
Wani abu da yanzu kasashen duniya suka kasa shawo kansa shi ne rikicin kasar Siriya, kuma ko da a jawabin da Merkel ta yi gaban majalisar dokoki, za a fahimci cewa kusan dai babu wata mafita ga rikicin na Siriya da yake kara zubar da jini. A wani abu wanda ba a cika samu a jawaban shugabannin Turai ba, a wannan karon tun da farko a jawabin nata shugabar gwamnatin Jamus ta tabo irin kokarin da suke yi na kyautata huldarsu da kasashen Afirka. Wani abu da ya fito fili a jawabin na shugabar gwamnatin Jamus, shi ne cewa duk irin bakin jini da kuma sukar da gwamnatinta ke ci gaba da fuskanta, ba ta da niyyar sauya ra'ayinta kan batun karbar baki ko da kuwa hakan zai yi illa ga kujerarta.