140611 Merkel ILO
June 15, 2011Mafita ga matsalar tattalin arziki
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da buƙatar ga ƙasashe su ɗauki salo iri na Jamus na kyautata dangantaka tsakanin ma'aikatan ƙodago da hukumomin ɗaukar ma'aikata, ta na mai cewa ta hakan ne kawai za'a kare haƙƙi da martabar aikin da kuma samar cigaba mai amfani. Merkel ta yi wannan jawabin ne yayin babban taron ƙungiyar ƙodago ta duniya a Geneva.
Shugabar gwamnatin ta Jamus ta kuma baiyana ƙudirin gwamnatin na ƙarfafawa matasa ƙwarin gwiwa waɗanda ke fafutukar wanzar da dimokraɗiyya a ƙasashen arewacin Afrika ta hanyar basu horo da za su iya samun ayyukan yi.
Ko can ma dai kafin ta gabatar da jawabin na ta, shugabar ta Jamus ta sami gagarumar tarba cikin murna da annashuwa daga wakilai, yayin da take wucewa zuwa zauren taron inda wasu daga cikin mahalartan suka miƙe tsaye suna yi mata tafi da jinjina wanda ba'a saba gani ba a taro irin wannan.
Kamar yadda ta faɗa da farko Angela Merkel ta ɗauki tsawon lokaci ta na bayanin matakan da Jamus ke ganin mafita ga matsalolin tattalin arziki da na harkokin hada- hadar kuɗaɗe, inda ma ta yabi matakan da kamfanonin Jamus suka ɗauka a lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki, ta na mai cewa matakin rage sa'oin aikin ma'aikata a wannan lokaci maimakon rufe masan'antun ya taimaka ƙwarai kuma ya zama abin koyi ga sauran ƙasashe.
Darasi abin koyi daga matakan Jamus
Ta ƙara da cewa irin nasarar da Jamus ta samu abu ne mai sauƙi, wannan kuwa shine ta haɗin kai da fahimtar juna tsakanin ƙungiyoyin ƙodago da hukumomin ɗaukar ma'aikata da kuma gwamnatoci. A saboda haka ta yi kira ga majalisar ƙodagon wadda ta ƙunshi dukkan waɗannan rukunai daga ƙasashe kimanin 183 da cewa
" Akwai darasi da ƙasashen duniya za su koya musamman wajen haɗin kai, ta fannin kyautata jin daɗi da walwalar jama'a, haka ma dai a lokacin wadata da bunƙasar tattalin arziki, da zuba jari a lokacin da ake fama da mawuyacin hali domin haɓaka cuɗanni in cuɗeka".
A waje guda kuma shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta yi kiran ƙarin haɗin kai daga ƙasashen arewacin Afirka da kuma ƙasashen larabawa waɗanda a yanzu suke fuskantar zanga zangar matasa dake neman 'yanci " Akan hake ne ma Jamus ke son bada gudunmawa ta wannan fuskar wanda muka kira yarjejeniyar taimakon ayyukan yi. Akwai yiwuwar a ƙarƙashin wannan tsarin matasa da dama za su sami horo wanda bayan sun kammala za su sami ayyukan yi a ƙasashensu. Jamus da Faransa za su gabatar da wannan tayi a lokacin taro mai zuwa na ƙasashe 20 masu cigaban masana'antu G20. Merkel ta ce akwai jan aiki a gaban gamaiyar ƙasa da ƙasa ta na mai cewa matakin bada shawara kaɗai ba zasu wadatar ba.
Haɗin kai da fahimtar juna domin cigaba
" Haƙiƙa wajibi ne mu ga cewa mun bi sahun shawarwarin da aka tattauna da ƙasashen ƙungiyar ta G20 yadda ba za su zamo batutuwan kasuwanci na fatar baka ba. Ko da yake harkokin kasuwannin kuɗaɗen suna da muhimmanci amma akwai buƙatar jama'a su fahimci muhimmancin al'amuran da kuma tasirinsa ga cigaban su".
Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta ce ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da suka haɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya da asusun bada lamuni na duniya da ƙungiyar raya tattalin arzikin nahiyar turai OECD da ƙungiyar ciniki ta duniya da kuma ƙungiyar ƙodago ta ƙasa da ƙasa suna da muhimmiyar rawa da za su taka.
" Ta ce kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro bayan yaƙin duniya na biyu haka zalika yake da muhimmanci a tabbatar da haɗin kai da taimakekeniya a tsakanin ƙasa da ƙasa da samar da daidaito da bunƙasar tattalin arzikin ƙasashen duniya.
Ana iya sauraron sautin wannan rahoto idan aka duba daga ƙasa.
Mawallafa:Malte Pieper/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmed Tijani Lawal