Ana fuskantar karancin yara masu zuwa makaranta a duniya
September 1, 2022Talla
Hukumar raya limi Kimiya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya Unesco, ta ce akwai kaso 40 cikin dari na yaran da ba sa zuwa makaranta a kasashen Kudu da Hamadar Sahara, kana Najeriya na kan gaba inda fiye da miliyan 20 ba sa da zarafin zuwa makaratu a kasar.
Wasu kasashen da suka hada da Habasha da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Kenya na daga cikin kasashen da gwamman miliyoyin yara da ba su zuwa makarantun boko a nahiyar in ji hukumar Unesco.
Sai dai akwai dan ci gaba idan aka kwatanta da na shekarar 2000 da suka gabata da ta gabata, duk da yake hukumar ta ce bai taka kara ya karya ba.