Ministar tsaron Jamus ta ajiye mukaminta
January 16, 2023Tun bayan da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kafa gwamnatinsa ne, ya nada Christine Lambrecht a matsayin ministar tsaro. Amma a cikin bayanan da ta wallafa a shafin nata na Facebook Lambrecht ta nunar da cewa: " Tsawon wata guda kafafen yada labarai suka kwashe suna mayar da hankali kan abin da ya shafi rayuwata, ya sanya da wahala muke bayar da kula ga jami'an tsaronmu da sojojinmu na Bundeswehr da ma batun tsare-tsaren tsaro da abin da ya shafi rayuwar al'ummar Jamus. Tilas a sanya ayyukan da sojojinmu da sauran jami'an tsaronmu ke yi tukuru, a sahun gaba. Hakan ta sanya na yanke shawarar ajiye mukamina, domin wani ya karbi ragamar."
Mai shekaru 57 a duniya, Lambrecht na shan suka musamman kan batun gaza inganta ayyukan rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr duk da makudan kudin da gwamnati ta warewa domin inganta ayyukan nasu. Tun dai bayan da Rasha ta mamaye Ukraine cikin watan Fabarairun 2022 ne, gwamnatin Jamus ta amince da ware makudan kudade na Euro domin bunkasa ayyukan rundunar sojojin. Muhawara kan karfin rundunar tsaron Jamus din ta Bundeswehr ta fara kamari ne cikin watan Disamabr bara, bayan da aka gaza yin aiki da tankokin yaki masu yawa a yayin atisayen sojojin kasar.
Lambrecht na shan suka kan balaguro da danta
A jawabinta na sabuwar shekara da ta gudanar, Lambrecht ta bayyana 2022 a matsayin shekara mai tarin kalubale, tana mai cewa: "Yaki na gudana a tsakiyar Turai, ina sane da abubuwa masu tarin yawa da suka wakana a dangane da yakin. A saboda da hakan, ina son mika godiyata a gare ku. Zan gudanar da bikin sabuwar shekara da iyali da abokaina, duk wadanda ba za su iya hakan ba saboda suna kare kasarmu da sauran bangarori, ina mika godiya ta musamman gare ku."
Wannan jawabin ya janyo mata suka daga kafafen yada labarai da kuma ‘yan adawa, wadanda ke zarginta da yin bayani a kan yakin yayin da ake bikin sabuwar shekara da wasan wuta a kusa da ita, abin da ke hada yanayin jin dadin da take ciki da kuma halin yakin da ake fama da shi a Ukraine. Ko cikin watan Afrilun bara ma dai, ministar ta sha suka sakamakon yin bulaguro da danta mai shekaru 21 a duniya cikin jirgin yakin sojoji.
Murabus din Lambrecht na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ke fuskantar matsin lamba kan batun taimaka wa Ukraine da kayan yaki ta hanyar amincewa da aike mata da manyan tankokin yaki kirar Leopard. A farkon wannan wata na Janairu ne, Jamus ta aike da kayan yaki da suka hadar da tankoki da makaman kare kai daga makamai masu linzami ga Kyiv.
Olaf Scholz ya amince da murabus din Lambrecht
Tuni shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz ya amince da murabus din na Lambrecht. Yayin wani taron manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin Christine Hoffmann ta bayyana cewa: "Kamar yadda kuka sani, ministar tsaro Christine Lambrecht ta bukaci shugaban gwamnati ya amince da murabus dinta. Shugaban gwamnatin, ya girmama ra'ayinta tare da gode mata kan kyakkyawan aikinta a lokacin da ake fama da tarin kalubale. Zai kuma mika sunan wanda zai maye gurbinta ga shugaban kasa cikin lokaci kankani."
Sai dai ta shaida wa manema labaran cewa, ba za ta iya sanar da lokacin da za a mika sunan magajin na Lambrecht ba. Tuni dai jam'iyyun adawa suka fara nuna bukatar gaggauta sanar da wanda zai gaje ta, inda wasu kafafen yada labaran kasar suka ruwaito sunayen wadansu mutane da ake sa ran guda daga cikinsu ka iya gadon mukamin na ministan tsaro.