EU za ta tattauna kan horas da sojin Ukraine
August 30, 2024Ministocin tsaron Tarayyar Turai sun hallara a Brussels babban birnin Belgium a ranar Juma'a domin tattauna batun ci gaba da bai wa sojin Ukraine horo don su tsare kasarsu daga mamayar Rasha.
Za su tafka muhawara kan ko za a koma horas da sojin na Ukraine cikin kasarsu ko kuma a'a. A halin yanzu ana horar da sojin Ukraine din ne a kasashen Jamus da kuma Poland sannan an fara horon ne a 2022.
Taron ministocin tsaron ƙungiyar EU a Portugal
A cewar alkaluman EU ya zuwa watan Mayun shekarar 2024 an horas da soji dubu 52 sannan ana ci gaba da aikin horon.
Kungiyar ta EU ta kuma nuna bukatar sake horas da karin sojoji dubu 60 kafun karshen kakar 2024 kuma ministocin tsaronta na neman a kara wa'adin horon zuwa 2026.
Rasha ta aikewa Nijar makaman kakkabo jiragen yaki da sojoji
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kuma kasar Lithuania na masu ra'ayin a horas da sojin na Ukraine cikin kasarsu maimakon wasu kasashen Turai.