Rasha ta aikewa Nijar makaman kakkabo jiragen yaki da sojoji
April 12, 2024Rasha ta aikewa Jamhuriyar Nijar makaman kakkabo jiragen yaki na sama da kuma kwararrun sojoji 100 da za su bai wa sojojin Nijar din horo na musamman kan dabarun yaki.
Karin bayani:Shugaba Tchiani ya yi magana da Putin
Gidan talabijin din Nijar RTN ya ruwaito cewa ma'aikatar tsaron Rasha na cewa za ta kafa na'urori daban-daban da sauran dabarun aikin soji a Nijar din don ita ma ta ci moriyar sojin bayan ta basu horon a nan gaba.
Karin bayani:Nijar: Sabon babin hulda da manyan kasashe
Wannan wani ci gaba ne da aka samu bayan tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Vladmir Putin na Rasha ya yi da takwaransa na Nijar Janar Abdourahamane Tchiani a karshen watan Maris din da ya gabata, inda suka tattauna a kan batutuwa da dama da suka shafi karfafa dangantakar diflomasiyya.
Tun bayan hambarar da gwamnatin dimukuradiyya a cikin watan Yulin bara, sojojin suka rinka katse alaka da kasashen yamma, ciki har da uwargijiyarsu Faransa sai Amurka, yayin da kuma babu tabbas kan yadda alakarsu da Jamus za ta kasance a nan gaba.