Muhammadu Sanusi II ya dawo sarautar Kano
May 23, 2024Bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta sake yi wa dokar masarautun jihar gyaran fuska a cikin gaggawa, daga karshe mahukuntan jihar Kano sun sake dawo da Muhammad Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano.
Wannan na zuwa ne bayan dogon lokacin da aka kwashe ana jita-jitar hakan za ta faru, kana tuni 'yan majalisa na jam'iyyar adawa ta APC suka yi watsi da sabuwar dokar da suka ce za ta kuntata wa mutanen karkara wadanda tun da farko tsohuwar gwamnatinsu ta ce ta rarraba masarautar domin su.
Karin bayani : Kirkirar masarautu a Kano ta haifar da mahawara
Yadda ta kaya a majalisar dokokin Kano
Kunshin dokar bashi da wani dogon turanci domin karara ya bayyana cewar a koma gidan jiya (ma’ana dai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya) inda aka ajiye dokar nadin sabbin sarakuna wacce aka yi ta ranar biyar ga watan Disambar 2019, da kuma wacce aka yi a ranar takwas ga watan Mayun shekarar 2019, wato dokokin da suka nada sabbin sarakuna hudu da kuma sauke sarkin Kano Muhammad Sunusi II.
Karin bayani : Sanusi Lamido Sanusi sabon sarkin Kano
Masu mukamai a masarautar Kano na cikin damuwa
Alhaji Aminu Babba Dangundi shi ne sarkin Dawaki Babba a masarautar Kano, guda daga cikin manyan masu rike da sarautun da wananan doka ta yi awon gaba da kujerun su, ya ce abin bai yi dadi ba kuma ba za su amince ba.
Ana tsaka da muhawara a kan dokar sai yan majalisar jamiyyar adawa ta APC suka fice daga majalisar tare da fatali da matakin dokar.