1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kano: Halin da ake ciki bayan tube Sarki Sanusi

Uwais Abubakar Idris
March 10, 2020

A Najeriya ana ci gaba da mayar da martani biyo bayan tsige mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi bayan shafe tsawon lokaci ana sa-in-sa a tsakanin sarkin da gwamnan jihar.

https://p.dw.com/p/3Z9y4
Sanusi Lamido Sanusi Gouverneur Zentralbank Nigeria
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/Getty Images

Wannan mataki da gwamnatin jihar Kanon ta dauka na zama tarihi da ke ci gaba da maimaita kansa tun daga lokacin da Najeriyar ta samun ‘yancin kanta, domin shugabanin siyasa da suka kai ga madafan iko sun kasance masu amfani da ikon da suke ganin doka ta ba su na nadawa ko tsige sarakuna a Najeriya.

Tsige tsohon Sarkin na Kano Muhammadu Sanusi na 11, ya zo a daidai lokacin da ake magana a kan batun dokokin Najeriyar da tanadin da suka yi a kan wannan, musamman batun cusa siyasa a daukacin al’amura na sarakuna da suke shugabanin alumma. Tuni dai tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a wasika ta musamman da ya rubutawa tsohon sarkin na Kano, ya ce tsige shi da aka yi bai dace ba, sai dai yana masa murna bisa matakin da ya dauka na sadaukar da kai ga kasa a tafarkin da ya zama.

Sarakunan gargajiya sun dade suna neman a sama masu madafa a tsarin mulkin Najeriya da za ta iya kai ga sauya musu a yayin da tsohon sarkin Kanon Sanusi na biyu ya fara zaman gudun hijirara da aka tilasta masa a garin Loko na jihar Nasarawa da ke a yankin tsakiyar Najeriya.