1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan dokar hana kara aure

February 21, 2017

Malamai da sauran al'umma na kace-nace bayan da sarkin kano Muhammadu Sanusi na biyu ya yi kira da a yi dokar hana wa marasa karfi kara aure bisa l' akari da yadda ake zubar da mata da 'ya'ya ba tare da kulawa ba.

https://p.dw.com/p/2XyXH

Yawaitar aure barkatai da sakin mata na daga cikin batutuwan da ke kawo gararambar kankanan yara a titi da kuma tallace-tallace ba tare da wata tartibiya ba. Wadanman da wasu dalilai ne suka sa sarkin kano Muhammadu Sanusi na biyu ya kafa kwamiti domin fitar da dokar da zata haramta wa duk wani marar sukuni kara aure.

,Amma Malaman addini sun rabu gida biyu a kan wannan doka tun ma kafin a dabbakata. Murtala Adam malamin addinin Musulunci mai mata hudu ya ce wannan yunkuri na yada fasadi ne a bayan kasa ta hanyar kwaikwayon Tuarawa. Sai dai Dr Zahrau Umar malama a sashen ilimin addinin Musulunci na jami'ar Bayero ta kano ta ce maganar ta sarki tana kan gaba koda kuwa a mahangar addini ne.

Wani magidanci mai suna Adam Mohammed wanda kuma kwannan ya angwance da amaryarsa karo na 2 ya ce sam wannan doka ba abu ne mai yiwuwa ba, gara ma a sauya tunani. Sai dai kuma a ra'ayin Abubakar Ibrahim mai sharhi kan al'amuran yau da kullum wanda ke da mata biyu ya ce maganar sarki bisa hanya take duba da barazana da ake fuskanta.