Martani kan yanayin tsaro
April 12, 2023Fadar Shugaban kasar dai na ganin ta yiwa Yan Nigeria Iyaka kokarin ta wajan murkushe aika-aikar Yan ta'adda ta kowanne bangare sai dai Kalaman sunzowa Al'ummar jahohin Arewa mason yammacin Kasar cikin bazata musamman jihar Zamfara da yanzu haka ke jimamin sace masu mutane 85. Comrade Jamilu Aliyu Charanci shine Shugaban kungiyar mutanan arewacin kasar yana ganin kalaman akwai yaudara saboda ana ci gaba da kai hare-hare da ke halaka fararen hula da garkuwa da mutane.
Mutanen da ke zauna a irin ayankunan dake fama da hare-haren 'yan bindiga irin su Bala Yaro mada sun bayyana halin da ake ciki gwamma jiya da yau. Haka sauran mutane a jahohin na Katsina da Zamfara na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan kalaman fadar Shugaban Najeriya wadanda suke gani suna cikin tsaro llokacin da shugaban ya dauki madafun iko a 2015.
Mafi akasarin mazauna jahohin sun bayyana fata kan samun sauki lamura idan aka rantsar da sabuwar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu mai jiran gado, wanda zai karbi ragamar tafiyar da kasar daga ranar 29 ga watan gobe na Mayu.