Muhawara kan kai El Zakzaky neman magani
August 6, 2019A yayinda hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya ta sanar da aiki da umurnin kotu da ta ba da izinin tafiya kasar Indiya don neman magani ga Shugaban Kungiyar ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, yanayin da za’a tafi da shi kasar bisa rakiyar jami’an tsaro a yanayin na diplomasiyar kasa da kasa da ma hallacin yin haka na zama abin dubawa.
Irin yadda hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriyar ta yi maza wajen sanar da cewa za ta mutunta umurnin kotu a kan ba da izini ko beli na tafiya neman magani ga shugaban na ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ya jefa kyakkyawan fata na fara samun sauyi a kan wannan batu da ke daukar hankali sosai. To sai dai sharuddan da ta gindaya bisa cewa jami’an tsaro ne zasu yi mashi rakiya zuwa kasar Indiya ya sanya tambayar ko akwai wannan bisda tari na diplomasiyar kasa da kasa.
Duk da cewa har yanzu akwai abubuwa da dama da suke lullube a kan wannan batu, domin babu cikakken bayani shin wanene zai daukin nauyin kudin kai shi asibitin a wannan yanayi da ake ciki. Akwai batu na bisa tsari na tsaron kasa da kasa, ko a tsari na ma’aikatar leken asiri akwai wannan?
Na yi kokarin jin ta bakin ofsihin jakadanci kasar Indiya a Najeriya wadanda sune za su ba da takardar izinin tafiya kasarsu, da ma hukumar tsaro ta farin kaya wacce ta bayyana mutunta umurnin kotu amma abin ya faskara.
Wannan ne dai karon farko da Najeriya ta mutumta hukuncin kotu a kan Sheikh Ibrahim Elzakzaky tun daga 2015 da ake tsare da shi, abin da masharhanta ke cewa zai yi tasiri sosai wajen sulhunta wannan batu, wanda bayanai suka tabbatar cewa sarakunan gargajiya da wasu tsaffin shugabanin Najeriya sun kai ga sa baki. Za a sa ido a ga yadda za ta kaya a kan batun.