Muhimmancin layya a addinin musulunci
August 10, 2019Layya sunna ce mai karfi a wurin mafi yawancin malamai na musulunci. Sunna ce ta manzon Allah S.A.W. tana da asali tun daga Annabi Ibrahim Alaihi salam. Annabi ya kwadaitar da a yi ta, shi kansa ya yi, ya kuma yi kira ga al’umma su yi.
Ana yin layya da dabbobi nau’in Rakumi da nau’in shanu da nau’in Awaki, wato Tunkiya da Akuya da Rago.
A cewar malamai idan rakumi ne ana son wanda ya kai shekara biyar. Idan kuma shanu ne ana son wanda ya girma ya kai shekara biyu. Idan kuma bangaren Awaki ne ana so a yi layya da wanda ya cika shekara daya ya shiga ta biyu.
Siffofin dabbobin da za a yi layya da su kuwa sune wadanda basu da larura, ba gurgu ba. Idan rago ne wanda kahonsa bai karye ba, sannan kunnensa bai tsage ba, kuma kafarsa bata karye ba sannan kuma ba ramamme ba.
Ana yin layya a ranar Idi da kuma kwanaki biyu na bayan idi