Ranar harshen uwa ta duniya
February 21, 2024Ana dai fuskantar matsaloli da dama, sakamakon yadda wasu manyan harsuna kan mamaye kanana har ya kai ga bacewar su a bayan kasa. Ana alakanta wadannan matsalolin da yadda wasu kabilu kan yi watsi da harshensu na gado, tare da rungumar wanda ba nasu ba. Jihohin Plateau da Taraba da wani bangare na jihar Kaduna da ke Tarayyar Najeriya, na daga cikin jihohi da ke da manya da kananan kabilu dabam-dabam. Ga misali a jihar Plateau bincike ya nuna akwai kabilu fiye da 40 wadanda ke magana da harsunansu, to amma sakamakon yadda wasu kabilun ke watsi da nasu harsunan na asali wasu manyan harsuna na kokarin mamaye. Wannan ya janyo wasu kananan harsuna na neman bacewa, don haka Hukumar UNESCO ke bayar da muhimmanci ga wannan rana ta harshen uwa domin gudun bacewar kananan harsunan a duniya.