Mummunan harin bam a Kano
July 30, 2013A daren ranar Litinin ne wasu bama-bamai da suka tashi a unguwar Sabon Garin Kano suka haddasa rasuwar mutane da dama bayan wasu da suka jikkata. Rahotanni sun tabbatar da cewar zuwa ranar Talata da rana akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu. An dai dauki tsawon lokaci a jihar Kano ba tare da samun wani tashin hankali ba. Wannan hari dai yayi kama da wanda kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram ke kaiwa, ko da yake har zuwa wannan lokaci babu kungiyar da ta ayyana daukar alhakin kai harin.
Tun da misalin karfe tara na daren ranar Litinin ne aka fara jiyo karar fashewar wani abu mai kara da ake kyautata zaton bam ne a unguwar New Road dake Sabon Garin, daga bisani kuma aka sake jiyo wata karar mai karfi wadda daga bisani aka tabbatar da cewar wasu bama-baman ne suka sake tashi a unguwar Enugu Road dake wannan yanki na Sabon Gari.
Sau hudu aka ji karar tashin bam
Wasu da suka shaida wannan al'amari sun bayyana cewar sau hudu ana jiyo karar fashewar wadannan bama-bamai, wadanda suka haddasa rasuwar mutane da dama baya ga wasu da suka jikkata.
Jim kadan bayan faruwar harin ne jami'an tsaro suka ringa diban gawarwaki da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin dake jihar ta Kano. Asibitin Murtala shi ne babban asibitin da aka fi kai wadanda harin ya rutsa da su, ya kasance cike da gawarwaki da kuma wadanda suka jikkata.
Garzawa asibiti don neman karin bayani
Wani matashi dake cikin rukunin wadanda suka je domin duba 'yan uwansu ya bayyana cewar harin ya rutsa da dan uwansa ko da yake dai bai rasa ransa ba amma ya jikkata.
Basiru Iliyasu magidanci ne da shi ma ke rukunin wadanda suka halarci asibitin domin ganin abin da ya faru, yayi harin haske a kan abin da ya gani da cewa bai taba ganin mummunan abu na rashin imani irin wannan ba.
A nata bangaren rundunar sojin Najeriya a jihar Kano ta tabbatar da faruwar harin ta bakin kakakin ta Captain Ikedechi Iweaha, sai dai bai yi wani karin haske ba.
Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Mohammad Nasiru Awal