Mutane 10,000 sun bace a Libiya
September 13, 2023Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na aiki ne da kungiyoyin agaji na cikin gida da kuma na kasa da kasa domin kai daukin gaggawa ga wadanda ke yankunan da iftila'in ya shafa a Libiya. A yanzu haka dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.
Karin bayani: Guguwa da ambaliya sun kashe rayuka a Libiya
Kungiyoyin bayar da agaji sun ce, ana neman wasu mutane kimanin dubu goma da suka bace sakamako mummunar guguwar ta Daniel. Ministan harkokin cikin gida na kasar ya tabbatar da mutuwar mutane fiye da 5,200.