Kifewar kwale-kwale ta halaka Mutane 8 a Mozambique
April 16, 2024Mutane 8 'yan gida daya sun mutu bayan da kwale-kwalensu ya kife a kasar Mozambique, kamar yadda gidan Rediyon kasar ya sanar a Talatar nan, inda ake ci gaba da laluben sauran mutane biyun da suka bace.
Karin bayani:'Yan ci ranin Sudan 13 ne suka mutu bayan kifewar kwale-kwalensu a gabar ruwan Tunisiya
Hatsarin ya faru ne ranar Litinin a kogin Zambezi, mako guda da faruwan wani mummunan hadarin jirgin ruwan da ya hallaka mutane 98, yawancinsu kananan yara a kasar.
Karin bayani:Kwalekwalen dauke da fasinjoji ya kife a Najeriya.
Mutanen dai sun cika jirgin ne fiye da kima, a kokarinsu na ficewa daga yankinsu mai fama da annobar kwalara, amma sai jirgin ya kife da su.
Bayan faruwar hatsarin na ranar 8 ga Afirilun nan, shugaba Filipe Nyusi ya ayyana zaman makoki na kwanaki 3 don nuna jimamin asarar rayukan mutanen su kusan 100 da suka mutu.